Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Ganduje, ya aike da sunayen sabbin kwamishinoni Takwas ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da babban mai taimaka wa kakakin majalisar dokokin, Isa Ɗan Abba, ya fitar yau Litinin.

Sanarwar ta ce gwamnan ya aike da sunayen mutum Takwas ɗin ne domin a tantance su kafin naɗa su kujerun kwamishinoni a gwamnatinsa.

An ruwaito cewa a zaman majalisar na yau Litinin, kakakin majalisar, Injiniya Hamisu Chidari, ya karanta sunayen da ke ƙunshe a takaradar da gwamnan ya aike musu.

Sanarwar ta ce gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya tura sunayen mutum Takwas da ya zaɓa domin tantance su da tabbatar da su a matsayin sabbin kwamishinoni.

Ɗan Abba ya bayyana sunayen mutanen da gwamnan ya zaɓa don naɗa su kwamishinonin kuma ya tura ga majalisa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.

Mutanen sun haɗa da, Alhaji Ibrahim Ɗan’azumi Gwarzo, Abdulhamid Abdullahi Liman, Hon. lamin Sani Zawiyya da Hon. Ya’u Abdullahi ‘Yan Shana.

Sauran kuma su ne; Honorabul Garba Yusuf Abubakar, Dakta Yusuf Jibrin Rurum, Hon. Adamu Abdul Panda, da kuma Alhaji Sale Kwasaimi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: