Rundunar ƴan sandan jihar Nassarawa ta tabbatar da sace wani kwamishina a jihar.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Ramhan Nansel ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai yau a Lafiya.
Ya ce ƴan bindiga sun yi garkuwa da kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na jihar Yakubu Lawal a daren ranar Litinin wayewar yau Talata.

Ƴan bindigan sun yi ta habe-harbe yayin da su ka je ɗaukar kwamishinan a ƙaramar hukumar Nassarawa-Eggon.

Tuni aka aike da jami’an tsaro don ganin an kuɓutar da wanda aka yi garkuwa da shi.
Ko a ranar Asabar sai da ƴan bindiga su ka kai hari wata makaranatar sakandiren kimiyya a ƙaramar hukumar Nassarawa- Eggon tare da hllka mutum guda.
Rundunar ta buƙaci jama’a da su taimaka musu da bayanai a kan wanda aka sace don ganin an kuɓutar da shi.