Rahotanni daga wasu kafafen yada labarai a Najeriya sun nuna cewar Sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau na shirin ficewa daga jam’iyyar NNPP.

Jaridun sun ce Malam Ibrahim Shekarau na ahirin komawa jam’iyyar PDP bayan ficewarsa daga NNPP.

A na zargin cewar ficewar Sanata Shekarau na da alaka da wasu manyan alkawura da ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya yi masa.

Daga wani ɓangaren an jiyo cewar wasu daga cikin jiga-jigar jam’iyyar NNPP sun buƙaci ganin Malam Shekarau domin ganawa da shi sai dai hakan ba ta yuwu ba.

An jiyo wani batu da ke nuna cewar ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP na neman Sanata Shekarau da ya koma jam’iyyar.

Ana zargin cewar Sanata Ibrahim Shekarau zai fice daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar PDP a yau Talata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: