Dakarun sojojin Operation Sanity sun kara kashe wasu yan bidiga a wata arangama da sukayi a dajin gulbe dake karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna.

Hakan na zuwa ne bayan kwanaki uku da sojoji suka kashe wasu yan bidiga da yawa.

A water sanarwa da kamfanin tsaro ma zaman kanta na Eons Intelligence, ta fitar a shafin na Tuwita a yau Talata, ta ce yan ta’adan sun gamu da karshen su ne yayin da suka zo kwashe gawarwakin yan uwan su da sojojin suka kashe ranar Asabar.

An rawaito labarin rahoton da gwamnatin jihar Kaduna ta fitar a ranar Asabar akan nasarar da dakarun sojoji sama da na kasa suka samu wajen kashe yan bindiga da dayawa a sabuwar atisayen dake suke gudanarwa a dazukan jihar.

Kwamishinan ma’aikatar tsaron na cikin gida, Mista Samuel Aruwan, ya fitar da sanarwar a ranar Asabar, inda ya ce an kashe ‘yan ta’addan ne a Galbi da ke karamar hukumar Chikun ta jihar.

Aruwan ya cigaba da cewa dakarun sojoji za su cigaba da gudanar da atisaye u duk wuraren da aka gano maboyan yan ta’adda ne a fadin jihar kaduna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: