Ma’aikatan muhalli a babban birnin tarayya Abuja sun yi barazanar rufe maƙabartun gwamnatin tarayya da ke Abuja.

Ma’aikatan sun rufe maƙabartar Gudu kuma bayan samun  matsin lamba daga fadar gwamnatin tarayya su ka buɗe a safiyar yau Alhamis.

Ma’aikatan sun fusata tare da koƙarin ɗaukar matakin ne sanadin rashin aiwatar da sabon tsarin albashi a tsakaninsu.

Wani shugaban ma’aikata mai suna Mukhtar Bala ya ce sun amince da buɗe wasu daga cikin maƙabartun ne tare da barazanar rufe maƙabartun Abuja baki ɗaya muddin ba a cika musu burinsu ba.

Shugaban ya nuna damuwarsa matuka a kan yadda a ke kin kulawa da bukatun ma’aikatan tare da watsi da su.

Shugaban ya ce matakin hakan sun ɗauka ne da yawun dukkan ƙungiyoyi baki daya wanda ya ce ko da a asibitoci ma su su ke kula da gawarwakin da ba a samu yanzu uwansu ba.

Ya ƙara da cewa sun fara rufe wasu maƙabartun ne bayan kiraye-kiraye da su ka samu daga fadar gwamnatin tarayya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: