Hukumar yada labarai a Najeriya, ta umarci gidan talabijin mai zaman kansa na Afrika, gidan talabijin na Silverbird da kuma kamfanonin yada labarai da gwamnatocin jihohi daban-daban ke tafiyar da su da su rufe ayyukansu cikin sa’o’i 24 masu zuwa saboda basukan da ake binsu da su ka kai akalla najra biliyan 2.6.

Babban Darakta a hukumar NBC, Balarabe Ilelah ne ya bayyana hakan ga manema labarai yau a hedikwatar hukumar da ke Abuja.

A cewar hukumar, duk gidajen talabijin da rediyon da abin ya shafa dole ne su dakatar da ayyukansu cikin sa’o’i 24 masu zuwa.

Hukumar ta ce kudaden da ake bi gidajen tashohin sun kai Naira biliyan 2.6, kuma wasu tashoshin da abin ya shafa ba su sabunta lasisin su ba tun shekarar 2015.

Ya ce Wannan shi ne kaso na farko, akwai wadanda ba su sabunta lasisi ba tun a shekarar 2015, 2016 da 2017, suna neman su zo su biya kudin lasisin.

Ya kuma yi gargadin cewa duk tashoshin da ba su sabunta lasisin su ba su gaggauta yin hakan nan da kwanaki 30 don kaucewa takunkumin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: