Hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Adamawa SEMA ta tabbatar da mutuwar mutane goma sannan wasu da dama sun bar muhallinsu a sakamakon mamakon ruwan sama.

Al’amarin ya faru a ranar Alhamis bayan da aka yi wani ruwan sama mai yawa da ƙarfi a ƙaramar hukumar Girie ta jihar.
Babban sakatare a hukumar bayar da agajin gagagwa a jihar Dakta Sulaiman Muhammad ya tabbatar da hakan ya ce ruwan saman ya sauka tsawon sa’o’i 15.

Sannan abin ya fi shafar mutanen ƙauyen Jabbi Lamba.

Dakta Muhammad ya ce mutane an samu nasarar gano gawarwaki shida daga cikin goma da su ka mutu yayind a ake ci gaba da laluben sauran gawarwaki huɗu.
Hukumar bayar da agajin gaggawa a Najeriya NEMA ta ziyarci wajen da lamarin ya faru a ranar Juma’a domin jin ƙan waɗanda lamarin ya shafa.
Bayan ziyarar hukumar ta gano cewar akwai gidaje da dama da su ka rushe sakamakon ruwan sama da aka yi mai yawa ranar Alhamis.