Ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam JNI ta yi kira ga gwamnatin tarayya da shugabannin hukumar sojin Najeriya don tabbatar da adalci a kan kisan babban malami a Yobe.

Hakan na cikin wata sanarwa da babban sakataren hukumar Dakta Khalid Abubakar Aliyu  da ya sanyawa hannu.

Snrwar ta ce wajibi ne a hukunbta duk masu hannu a ciki tare da bayyana hukunci a duniya domin ya zama izina ga na gaba.

Ƙungiyar ta nuna kaɗuwa a kan a dangane da kisan Sheik Goni Aisami wanda wasu sojoji su ka harbeshi tare da ƙoƙarin karɓe motarsa.

Sanarwar da aka fitar a madadin mambobinta na ƙasa sun yi Alla-wadai da kisan malamin wanda su ka siffantashi da cin amanar ƙasa.

Wasu sojoji sun hallaka Sheik Goni Muhammad Aisami bayan ya rage musu hanya  a jihar Yobe wanda hakan ya girgiza al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: