Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ASUU ta ce za ta dub yuwuwar janye yajin aikin da ta ke yi ko akasin haka a zaman da za ta yi da mambobin ƙungiyar ranar Lahadi.
Ƙungiyar za ta zauna da masu ruwa da tsaki a ƙungiyar a ranar Lahadi 28 ga watan Agustan da mu ke ciki.
Wani daga cikin mambobin ƙungiyar ya shaidawa jaridar PUNCH cewar ƙungiyar za ta gana da masu ruwa da tsakin ne a Abuja.
Hukumar za ta bai wa mambobinta damar tattaunawa a jihohi domin samar a matsaya ta ƙarshe a dangane da yajin aikin da ake yi.
Gwamnatin tarayya ta ce ta kammala samar da daidaito ga dukkanin matsalolin da ke tsakaninsu da ƙungiyar.
Sai dai gwamnati ta ce ba za ta bayar da damar biyan albashin malaman na watannin da su ka shafe su na gudanar da yajin aikin ba.
Idan ba a manta ba ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ta fara yajin aiki ne a ranar 14 ga watan Fabrairun shekarar 2022 domin jan hankalin gwamnatin ƙasar do cika musu alƙawuran da aka ɗaukar musu tsawon lokaci.