Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bayar da umarnin hukunta wadanda aka samu da hannu a cikin kisan Sheikh Goni Aisami na Jihar Yobe.

Mai magana da yawun Shugaban Malam Garba Shehu shi ne ya bayyana hakan ta cikin sanarwar da ya fitar.

Shugaban ya bayar da umarnin ne a ranar Talata bayan hallaka Malamin da batagarin sojoji su ka yi a ranar Juma’ar da ta gabata.

Sanarwar ta kuma bayyana yadda shugaban ya yi alla-wadai da yadda aka yi kisan gillar tare da bai wa rundunar sojin umarnin hukunta wanda aka samu da laifin.

Babban hafsan rundunar soji ya bayyana cewa an kama jami’in rundunar da ake zargi da hannu wajen kisan ya sabawa koyarwar rundunar.

Ya kuma ce hakan mummunan laifine aikatawa al’umma ta’addanci tare da sanya shukku a cikin zukatan su akan jami’an tsaro.

Ya ce aikata hakan da jami’in ya yi na iya shafawa rundunar bakin fanti tare da kin amincewa da su wajen taimaka musu a wasu al’amura a Najeriya.

Ya kuma bayar da izinin ga mahukunta a cikin rundunar da su hukunta dukkan wanda aka kama da hannu a cikin kisan tare da korar masu hali irin nasu a cikin jami’an

Leave a Reply

%d bloggers like this: