Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce yan takarar da ke karkashin jam’iyyar APC kaɗai zai marawa baya a zaben shekarar 2023.

Buhari ya bayyana haka ne a sanarwar da mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu ya sanyawa hannu ranar Laraba.

Sanarwar ta ce Buhari zai goyi bayan ƴan jam’iyyar ne a zaben shekarar 2023 kuma su kaɗai ba tare da goyon bayan wani ɗan takara daga wata jam’iyyar ba.

Ya ce hakan ba ya na nufin ya na suka ko kushe wani ɗan takara da ke wata jam’iyyar ba ne illa ganin ya mara baya har jam’iyyarsa ta samu nasara.

A yayin da ake tunkarar zaben shejarar 2023, wasu daga cikin yan jam’iygar APC na ficewa tare da samun tikitin takara a zaɓen da mu ke tunkara.

Daga cikin yan siyasar da su ka nemi tikitin takara a wasu jam’iyyun akwai makusanta ga shugaba Buhari da wasu da su ke da alaƙa ta ƙut da kut da shugaba Buhari.

Al’amuran siyasa a Najeriya na ci gaba da zafafa yayin da ya rage ƙasa da watanni bakwai a gudanar da babban zaɓen shekarar 2023.

Leave a Reply

%d bloggers like this: