Tawagar binciken sirri ta IRT dake karkashin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya, ta damke mai kai wa ‘yan bindiga bayanai da ya kai ga sace mata da ‘ya’ya biyu na Ibrahim Aminu, ‘dan majalisa a jihar Katsina.
Rundunar IRT tabayyana hakan a takardar da ta fitar a ranar Lahadi.
Yan bindiga sun kai farmaki gidan ‘dan majalisar dake wakiltar mazabar Bakori a majalisar jihar Katsina kuma suka yi awon gaba da matar da yara biyu a watan Satumban 2021.
Jami’an IRT dake aiki da Operation Restore Hope, sun ce sun yi aiki da bayanai gamsassu kuma suka kama wadanda ake zargin a maboyarsu daban-daban.
Manyan wadanda ake zargin sune Muttaka Ibrahim, Sulaiman Rabi’u da Surajo dukkansu maza kuma ‘yan asalin karamar hukumar Bakori.
An kama su kan zarginsu da ake yi da samar da bayanan sirri da suka kai ga garkuwa da iyalan ‘dan majalisar.
Kamar yadda takardar ta bayyana, Muttaka Ibrahim ya amsa laifinsa kuma ya karbi kudi N130,000 daga shugaban ‘yan bindigan sannan yace Yusuf Bala dake Zaria ne abokin aikinsa.
Ibrahim yace shi da sauran mambobin tawagarsa ne masu kai wa Sani Tukur bayanai wanda aka fi sani da Abacha, kuma ya kware wurin addabar mazauna jihohin Katsina da Zamfara.
A yayin bayanin abinda ya fuskanta ga ‘yan sanda, ‘dan majalisar yace ya biya kudi naira N37,500,000 ga shugaban ‘yan ta’addan domin karbar iyalan sa.


