Mazauna kauyen dan Gunu da ke Sarkin Pawa cikin karamar hukumar Munya ta Jihar Neja sun nuna bacin ransu dangane da yadda matsalar rashin tsaro ta ke kara tsanan ta a Jihar.

Mazauna kauyen sun nuna fushin su akan shugaban karamar hukumar ta Munya a Jihar, inda su ka bayyana cewa shugaban bai damu da halin da mazauna kauyen ke ciki ba.

Mazauna kauyen sun bayyana cewa akalla shugaban karamar hukumar Muhammad Garba Daza ya kwashe tsawon shekara daya bai kaiwa kauyen ziyara ba.

Inda su ka ce Hon Muhammad Garba Daza yana nuna wa kauyen halin ko in kula ga mazauna kauyen tare da kin taimakawa wadanda ‘yan bindiga su ka kaiwa hari a lokacin da su ka nemi taimakonsa ko kuma basu tallafi.

Sun ce ‘yan bindiga sun addabi kauyen na Gunu da kai hare-hare a cikin sa.

Bayan kokawa da mazauna kauyen su ke yi shugaban karamar hukumar su ka samu labarin zuwan sa kauyen domin yiwa wasu mutane ta’ aziyyar kashe musu ‘yan uwa da aka yi.

Bayan samun labarin zuwan Muhammad Daza da mazauna kauyen su ka yi hakan ya sanya wasu matasa su ka je gidan ta’aziyyar inda su ka bai wa shugaban izinin ya bar musu kauye.

Bayan umarnin da matasan su ka bai wa Shugaban daga bisani su ka fara jifansa domin ya fice daga kauyen harta kai ga sun fasa motocin tawagar sa guda hudu inda kuma jami’an tsaro su ka kubtar dashi.

Lamarin ya farune a karshen makon da ya gabata amma Shugaban Karamar hukumar bai ce komai ba akan lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: