Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya (NDLEA) ta kama wani mai shekara 53 mai bukata ta musamman, Ehiarimwiam Osaromo Emmanuel, a filin sauka da tashin na jiragen kasa da kasa da ke Murtala Muhammad da ke Ikeja a jihar Legas bisa zargin safaran miyagun kwayoyi.

Ehiarimwiam dai ya shiga hannu ne a ranar Lahadi 28 ga watan Agustan 2022 a lokacin da yake kokarin tafiya zuwa kasar Italy ta Doha a Jirgin Qatar Airways.
Kakakin NDLEA na ƙasa Femi Babafemi, ya ce dan asalin karamar hukumar Orhionmwon ta jihar Edo ya shiga hannu ne a lokacin da ya boye kwayar Tramadol samfurin 225mg guda 5,000 a cikin jakarsa.

Ya ce, tunda farko dai wanda ake zargin ya yi ‘yan dabarunsa da yake ganin zai iya boye wa jami’an hukumar kwayoyin da ya dauko amma sakamakon bincike da aka gudanar da aiki tukuru jami’ansu sun gano kwayoyin da ke dauke da su.

Ya ce yanzu haka suna cigaba da kokarin ganowa da dakile aniyar kungiyoyin da ke hadawa da rabar da sinadarin Crystal a sassan kasar nan.