Kungiyar kare hakkin musulmi ta Najeriya MURUC ta yi kira ga mahukuntan Jihar Ebonyi da su zurfafa bincike domin zakulo wadanda su ka hallaka malamin addini a Jihar.

Kungiyar ta bayyana cewa ana zargin ‘yan kungiyar IPOB ne su ka hallaka Malamin mai suna Sheikh Ibrahim Iyiorji a gidansa da ke garin Abacha na Jihar.
Kungiyar ta tabbatar da cewa malamin ya rasu a ranar litinin bayan kai shi Asibitin koyarwa na Tarayya da ke Abakaliki a Jihar.

Shugaban kungiyar ta MURUC reshen Birnin tarayya Abuja Salahudden Ustaz Yunus ya mika sakon ta’aziyyar sa ga gwamnatin Jihar da mazauna Jihar, inda kuma ya bukaci gwamnatin ta hukunta dukkan wanda aka samu da hannu a kisan malamin.

Kungiyar ta bukaci hukumomin Jihar da su zurfafa bincike domin kamo wadanda su ka aikata laifin domin yi musu hukunci.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Ebonyi ya bayyana cewa rundunar su ba ta samu labarin hallaka malamin da aka yi a jihar ba.