Dakarun Operation hadin kai sun samu nasarar kama wasu mutane biyu da ake zargin da taimakawa ‘yan ta’adda a Jihar Kaduna.

Daraktan yada labarai na rundunar Manjo Janar Musa Danmadami ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke bayyana irin nasarorin da jami’an rundunar su ka samu a watan Satumbar da mu ke ciki.
Jami’an sojin sun bayyana cewa sun kama mutanen ne a lokacin da su ke neman wani mutum mai suna Alhaji Abubakar wanda ya ake zargin sa da bai wa ‘yan bindiga tallafin kudade idan su ka bukata.

Danmadami ya ce an kama mutane ne wadanda ake zargi su na da alaka da wanda jami’an su ke nema a wani banki da ke garin Zariya yayin da su kaje cirar kudi.

Manjo Musa ya kara da cewa an kama mutane a ranar 15 ga watan Satumba a lokacin da su ke kokarin cire kudin fansa wasu mutane da aka tura asusun mutumin da su ke nema.
Darakta ya ce jami’an su su na ci gaba da gudanar da bincike domin kamo wanda su ke nema harma da wadanda su ke tallafa wa ‘yan ta’addan a yankin.