A na zargin gwamnatin jihar ta rufe wasu tashoshin watsa labarai a jihar ne bisa zargin ɗakko taron jam’iyyar PDP a jihar.

Al’amarin ya faru a ranar Asabar cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Ibrahim Dosara ya sanar.

Sanarwar da ya fitar ya ce gwamnatin jihar ta bayar da umarnin rufe tashoshin rediyo na Vision FM, Radio Nigeria Pride FM, Al’umma TV, NTA da Gamji Television.

A sakamakon haka ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa NUJ ta yi Alla-wadai da faruwar lamarin.

A wata sanarwa da sakataren ƙunguyar na ƙasa Shu’aibu Usman Leman ya sanyawa hannu, ya tabbatar da hakan a matsayin matakin da bai dace ba.

A ɓangaren ƙungiyar masu kafafen watsa labarai ta ƙasa BON ma cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren ƙungiyar Dakta Yemisi Bamgbose su ma sun yi turr da lamarin.

Haka zalika hukumar kula da kafafen yaɗa labarai ta ƙasa ta bayyana hakan a kan abu mara daɗi.

Zargin da ya fi ƙarfi shi ne ganin yadda kafofin watsa labaran su ka ɗakko yadda taron jam’iyyar PDP ya gudana a jihar kuma ake zargin hakan ya sa gwamnatin jihar ta rufe tashoshin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: