Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Edo, Kanal David Imuse Mai ritaya, ya yi kira ga gwamna Godwin Obaseki ya yi murabus daga kan kujerarsa.

Imuse ya yi wannan kiran ne yayin da yake martani ga kalaman da gwamna Obaseki ya yi ranar Juma’a cewa gwamnatinsa zata samu koma baya sakamakon za’a mayar da hankali kan harkokin yaƙin neman zaɓen shekarar 2023.
Shugaban APC yace idan Obaseki ya yi murabus zai bai wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) damar shirya sabon zaben gwamna a jihar, kamar yadda jaridar Punch ta rawaito.

A wata sanarwa da mataimakin kakakin APC a Edo, Ofure Osehobo, ya fitar ranar Lahadi, shugaban jam’iyyar Wanda ya jima yana sukar gwamnatin, yace kiran ya zama tilas saboda fargabar da mutane ke yi cewa gwamnatin ta tsaya cak.

Bugu da kari, ya yi ikirarin cewa tun kafin kalaman gwamna, Mutanen jihar Edo sun jima da barin Obaseki cewa dabaru da tunaninsa sun kare tun lokacin da aka rantsar da shi a zango na biyu.