Ƙungiyoyin A Kano Sun Bukaci A Sauya Ɗan Takarar Majalisar Tarayya Na Tudun Wada Da Doguwa

Wasu ƙungiyoyin siyasa a jihar Kano sun bukaci gwamna jihar Kano Abdullahi Ganduje da sauran jagororin jam’iyyar APC su sauya ɗan takarar majalisar tarayya na Tudun Wada da Doguwa.
Ƙungiyoyin masu rajij tabbatar da demokaraɗiyya, sun ce ba sa buƙatar irin Alasan Ado Doguwa a wakilcin zauren majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar Doguwa da Tudun Wada.

A wasiƙar daban-daban da ƙungiyoyin su ka aikewa gwamnan, sun ce ba irin Alasan Ado Doguwa su ke buƙata a wakilcin yankinsu a zauren majalisar wakilai ta ƙasa ba.

Ƙungiyoyin sun ce irin Alasan Ado Doguwa a wakilci, tamkar zubar da ƙimar jihar Kano ne a majalisa.
Ƙungiyoyin sun ce ɗan majalisar wakilai na Tudun Wada da Doguwa ba ya mutunta zaɓin gwamna ga yan takarar gwamna da mtaimakinsa a don haka ba sa buƙatarsa a majalisa.
A wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Malam Abba Amwar ya fitar, sanarwar ta ce ƙungiyoyin sun nuna rashin jin daɗi a bisa nuna rashin ɗa’a da Alasan Ado Doguwa ya nuna ƙarara.
A daren Litinin wayewar yau Talata ake zargin an samu saɓani tsakanin ɗan takarar mataimakin gwamnan Kano Murtala Sule Garo da Alasan Ado Doguwa.