Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar APC Kashim Shettima ya tabbatar da cewar za su magance dukkan matsalar tsaro da Najeroya ke fuskanta cikin watanni shida.

Ɗan takarar ya tabbatar da hakan yayin ganawa da ƙungiyoyin yan kasuwa a jihar Legas.
Ya ce tsarin shugabancin da su ka shirya da ɗan takarar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, sun shirya kawar da matsalar tsaro cikin watanni shida idan su ka kasance a kan karagar mulkin kasa.

Ya ƙara da cewa, za su tabbata sun ɗauki matasa aikin tsaro a ɓangaren soji, yan sanda da sauran jami’an tsaro.

Sannan za su tabbatar sun bayar da gudunmawa da kayan aiki ga jami’an tsaron Najeriya.
Idan ba a manta ba, jam’iyyar APC ta yi irin wannan alƙawari tun a lokacin yaƙin neman zaɓen shekarar 2015 kuma su ka sake maimaitawa a shekarar 2019.
Sai dai a yanzu, gwamnatin ƙasar bisa jagorancin jam’iyyar APC ta sha alwashin kawar da matsalar tsaro nan da watan Disamban shekarar da mu ke ciki.