Hukumar hana cin hanci da rashawa a Najeriya na aikin sa idanu kan wasu gwamnoni uku da ake zargi da handame maƙudan kuɗaɗe

Gwamnonin uku dake kan karagar ana zarginsu da ɓoye maƙudan kuɗi da su ka ɓoye.
Shugaban Hukumar yaki da rashawa, Abdulrasheed Bawa ya sanar da Daily Trust a zantawar da suka yi ta musamman a ranar Alhamis.

Yace samamen da suke kaiwa ‘yan canji zasu cigaba inda yayi kira ga ‘yan Najeriya da su goyi bayansu domin amfanin kowa.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, babban bankin Najeriya a ranar 26 ga watan Oktoban 2022 ya sanar da cewa kasar nan zata canza wasu takardun kudadenta domin dakile matsalolin tattalin arziki da suka addabeta.
Yayin da za a fara saki sabbin kudaden a ranar 15 ga watan Disamba, ‘yan Najeriya suna da dama har zuwa ranar 31 ga watan Janairun shekara mai zuwa don su kai tsofaffin kudaden su banki.
Sai dai kokarin da manyan ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, masu zuba hannayen jari da sauran jama’a ke yi na canza Naira zuwa daloli ya fara kawo matsala ga tattalin arzikin kasar.
A hirar da Daily Trust tayi da Abubakar Bawa, ya bayyana cewa wasu gwamnonin suna kokarin ganin sun killace kudaden da suka sata.
Yace a Yanzu haka suna kallon uku daga ciki.
Bawa wanda ya ki bayymana sunayen gwamnonin uku, sai dai ana zargin biyu daga cikinsu na yankin arewa yayin da dayan yake daga kudancin kasar nan.
Yace bayanan sirri da hukumar ta samu sun bayyana cewa gwamnonin sun kammala shirin zuba kudin ta hanyar biyan albashi da tsabar kudin wanda zasu ba ma’aikata a hannu.
Da aka tambayesa ko hukumar zata kira gwamnonin, shugaban EFCC yace suna dai sanye da idanu a kansu.