Hukumar hana cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta samu umarni daga kotu don karɓe ikon gidaje guda 40 na Ike Ekweremedu.

A na zargin Ekweremedu da mallakar gidajen ta haramtaciyyar hanya.

Alƙalin babbar kotun tarayya da ke Abuja Inyang Ekwo ne ya bayar da umarnin ga hukumar EFCC don karbe ikon gidajen na wani lokaci.

Gidajen da hukumar za ta jarɓe ikonsu na a jihar Enugu, da babban birnin tarayya Abuja.

Tuni akakama Ekweremedu a birnin Ingila bisa zargin cire sassan jikin wani yaro.

An kama Sanatan da matarsa a Landan yayin da su ke ci gaba da fuskantar shari’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: