Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai na tarayya, Alhassan Ado Doguwa, ya nesanta kansa daga wani rahoto da wata kafar watsa labarai ta intanet ta wallafa na cewa ya yi barazanar tonawa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano kan cire kudi daga albashin ma’aikatan kananan hukumomi a jihar, yana mai cewa labarin ba gaskiya ba ne.

Doguwa, cikin sanarwa da ya fitar mai dauke da sa hannunsa, ya ce Ganduje har yanzu shugabansa ne yana mai cewa rahoton da jaridar ta wallafa ba shi da tushe.

Doguwa ya bayyana rahoton a matsayin makirci, da makiya ‘masu hassada’ suka yi don bata masa suna da janyo rudani tsakaninsa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Doguwa ya ce lauyoyinsa za su dauki mataki a kan lamarin, yana mai cewa bai taba yin wani mummunan zato ga gwamnan ba, wanda ya bayyana a matsayin gwamna ‘mafi kwazo a jihar, ballanta ya yi maganar tona shi.

Doguwa ya ce yana cikin gwamnatin Ganduje wanda ya ce duk wani mutum mai tunani na gari a jihar zai yi alfahari da shi wanda ya kawo cigaba a dukkan bangarorin cigaban rayuwa.

Dan majalisar ya bukaci mawallafin labarin ya janye labarin ya kuma nemi afuwarsa, rashin hakan zai janyo ya dauki matakin shari’a a kai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: