
Tun biyo bayan alakar da tayi tsami tsakanin Shugaban masu rinjaye a majalissar wakilai ta kasa Alasan Ado Doguwa da Dan takarar mataimakin Gwamnan Jihar Kano Murtala Sule Garo dukka a jam’iyyar APC, ake alakanta Shugaban masu rinjayen da ficewa daga jam’iyyar.
Idan za’a iya tunawa a makon a farkon makon da muke ciki ne jiga-jigan Jam’iyyar APC din a jihar Kano suka samu sabani a tsakanin su, a yayin wani zaman tattaunawa na masu ruwa da tsaki a gidan Mataimakin Gwamnan Kano kuma Dan takarar Gwamna a Jam’iyyar APC Nasiru Yusuf Gawuna.

Saidai cewa a wani taron ganawa da magoya baya da Doguwan ya kira a Gidan sa a Daren ranar juma’ar da ta gabata ya bayyana alakar sa da tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso da cewa, babu wani sabani a tsakanin su illa kawai rashin yi masa ta’aziyyar rasuwar Mahaifin sa da Tsohon Gwamnan bai yi ba.

Rahotanni a yanzu haka sun bayyana cewa, tuni Tsohon Gwamnan Rabiu Musa Kwankwaso ya tura wakilai ga Alasan din domin yi masa ta’aziyyar, wakilan da suka hadar da Sanata Rufa’i Sani Hanga, Kabiru Alhassan Rurum, Shugaban Jam’iyyar NNPP Na Jihar Kano Umar Haruna Doguwa da kuma Sarki Aliyu Daneji.
A yayin ziyarar ta’aziyyar dai ana sa ran zasu jawo Hankalin Alasan Ado Doguwa, domin ya dawo izuwa jam’iyyar tasu ta NNPP.