Hukumar yaki da fasakwaurin miyagun kwayoyi, NDLEA ta damke wasu ‘yan kasuwar Fakistan a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad dake Legas dauke da kilogiram 8 na hodar iblis.

Femi Babafemi, mai magana da yawun hukumar NDLEA yace an boye miyagun kwayoyin ne a amsa kuwwa wacce wanda ake zargin yake kokarin hawa jirgin Qatar Airways zuwa Lahole, Fakistan ta Doha.

Yace mutum biyun da ake zargin sune Asif Muhammad da Hussain Naveed wadanda ke da katin zaman Najeriya kuma sun saba zuwa Najeriya kan kasuwancin tufafi.

Kamar yadda yace, an kama su a ranar Asabar a filin jirgin sama na Legas, kasa da mako daya bayan zuwansu Najeriya.

A daya bangaren, jami’an NDLEA dake Skyway Aviation Handling Company a ranar Juma’a sun kwace katan 13 na Tramadol 225mg da 200mg da aka shigo dasu daga Karachi, Fakistan. Babafemi yace kayan suna da nauyin 465.

NDLEA a cikin watannin nan yana cigaba da tsanantawa a bangaren yaki da fataucin miyagun kwayoyi kuma ana samun nasarori.

Leave a Reply

%d bloggers like this: