Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya samar da Sulhu a cikin jam’iyyar APC ta Jihar Kano, biyo bayan rikicin da ya barke kwanan nan a Jam’iyyar.

Rikicin ya barke ne a makon da ya gabata tsakanin Shugaban masu rinjaye a majalissar wakilai ta Kasa Alasan Ado Doguwa, da kuma Tsohon kwamishinan kananan Hukumomi kuma Dan takarar mataimakin Gwamnan jam’iyyar ta APC a Kano wato Murtala Sule Garo.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Alasan Ado Doguwa ya tabbatar da samuwar wannan sulhun ga wani Dan Jarida a Jihar ta Kano a safiyar wannan rana ta Talata.

Idan za’a iya tunawa an zargi dai Alasan din ne da Jifan Murtala Garo da kofin shan shayi, a yayin wani zaman tattaunawar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar. In da har aka ruwaito cewa ya ji masa rauni.

Saidai Shugaban masu rinjayen ya musanta Zargin, sannan kuma ya yi ikirarin cigaba da takun saka da Murtala har zuwa yanda hali zai yi.

Sai dai kuma a wani shirin siyasa na gidan Rediyo, an jiyo Doguwan ya bayyana cewa an sulhunta shi tare da Murtala, kuma Gwamna Ganduje ne ya jagoranci zaman Sulhun. Tare da wasu jiga jigan jam’iyyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: