Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi bayanin abin da ya sa Asiwaju Bola Tinubu zai yi nasara a zaben shugaban kasa da za ayi.

Buhari ya yi magana da gidan talabijin na kasa na NTA yayin da yake kasar Birtaniya, inda ya je a duba lafiyar jikinsa.
Da aka tattauna da shi a ranar Laraba, 9 ga watan Nuwamba 2022, Muhammadu Buhari yayi hasashen nasarar jam’iyyarsa ta APC ne a zaben 2023.

Shugaban kasar yake cewa Asiwaju Bola Tinubu zai lashe zaben shugabancin kasa saboda irin rawar da ya taka a lokacin da ya rike gwamna a Legas.

Buhari ya shaidawa gidan talabijin cewa har yau ayyuka da nasarorin da Bola Tinubu ya samu daga shekarar 1999 zuwa 2007 a Legas suna nan har yau.
A hirar da aka yi da shi, jaridar Nation tace shugaban Najeriyan ya bayyana ‘dan takaran kujerar shugaban kasar a matsayin gawurtaccen ‘dan siyasa.
Haka zalika shugaban kasar ya tabbatar da za ayi zaben adalci da gaskiya a shekara mai zuwa, yace zai so ya kafa wannan tarihin a kan gadon mulki.
A cewarsa, zai yi duk abin da zai iya wajen ya hana a shigo da kudi daga kasashen ketare domin ayi amfani da su wajen murde zabin da jama’a suka yi.
A nan ne ya yi magana a kan nasarar APC mai mulki a karo na biyu, yace jam’iyyarsa za ta kafa gwamnati bayan shudewar wa’adinsa a watan Mayun badi.