Shugaban kungiyar dattawan mabiya addinin kirista na arewacin Najeriya Oyinehi Ejoga ya bukaci mabiya addinin kirista da kada su kuskura su goyawa jam’iyyar APC baya a yayin zaben shekarar 2023 sakamakon nuna rashin kulawa da su ka yi dasu.

Ejoga ya bayyana hakan ne a yayin wata zantawa da yayi da manema labarai a taron kokin Zauren a ranar juma’a.

A yayin jawabin Prof Josaiah Onaolapo ya bayyana cewa zaben shekarar 2023 zai iya zama kalubale ga ‘yan Najeriya matukar ba a yiwa mabiya addinin kirista na arewa abin ya dace ba.

Taron wanda ya kasance mai taken siyasar yau mafita ga kiristoci ya ce ya zama wajibi mabiya addinin na kirista su shiga cikin siyasa a dama da su.

Onoalapo ya kara da cewa zaben da ya ke tunkarowa wata barazana ce ga mabiya addinin na kirista musamma a arewa muddin ba su yi abinda ya kamata ba.

Shugaban ya ce jam’iyyar ta APC ba ta yin abu akan tsari inda kuma ta yi watsi da mabiya addinin na kirista.

Kiristocin na yin hakan ne tun bayan da jam’iyyar APC ta tsayar da Kashim Kashatti a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar wanda wasu su ke ganin an yi shakulatin bangaro da mabiya addinin na kirista.

Leave a Reply

%d bloggers like this: