Kotun daukaka kara dake zamanta Abuja ta Tabbatar da sunan Bashir Machina, a matsayin Dan takarar sanatan Yobe ta Arewa a jam’iyyar APC.

A zaman kotun na yau Litinin, ta jaddada hukuncin da Babbar kotun tarayya tayi wacce take zamanta a Damaturu. Wacce tace Shugaban Majalissar Dattawa Ahmad Lawan ba shine halastaccen Dan takarar jam’iyyar ba a zaben shekara mai zuwa.

Mai Shari’a Monica Dongban-Mensen da ta jagoranci Alkalai uku, ta tabbatar da hukuncin a daukaka karar da Ahmad Lawan yayi na kalubalantar hukuncin Fadimatu Aminu ta Babbar Kotun tarayya dake Damaturu tayi.

A ranar 28 ga watan Satumbar da ya gabata ne dai, Mai Shari’a Fadimatun ta ayyana Bashir Machina amatsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin sanatan yankin na Jam’iyyar APC a zaman kotun.

A watan Mayun da ya gabata ne jam’iyyar APC ta gabatar da zaben fidda gwanin Sanatan Yankin Yobe ta Arewa, a lokaci da shi kuma Ahmad Lawan ya shiga zaben fidda gwanin Dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar da aka gudanar a watan Yuni.

Leave a Reply

%d bloggers like this: