Ana zargin wasu tsageru da ba’a tantance ba, sun cinna wuta a ofishin Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC dake karamar hukumar Izzi a jihar Ebonyi jiya Lahadi.

An tabbatar da hakanne a wata sanarwa da Shugaban kwamitin yada labarai da ilimantar da Al’umma akan harkokin zabe na hukumar Festus Okoye ya fitar.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, wannan shine karo na uku a ‘yan kwanakin nan da ake kai harin a ofisoshin kananan hukumomi na hukumar.

Idan za’a iya tunawa a cikin makonni ukun da suka gabata, an kai makamancin wannan harin a ofisoshin hukumar dake wasu kananan hukumomi a jihohin Ogun da Osun.

Al’amarin ya faru ne da kimanin karfe goma na safiyar jiya Lahadi, inda aka tarar da babban ginin ofishin da sauran kayayyakin dake ciki sun kone kurmus.

Abin da bayani ya tabbatar shine, Akwatunan kada kuri’u 340 ne suka kone da kananan rumfunan zabe 130. Sai Injinan Jannareta 14 da kuma Babban tankin Ajiyar ruwa da kuma sauran kayayyaki masu na hukumar.

A nata bangaren hukumar ta tabbatar da cewa, jami’an yan sanda sun gabatar da cikakken bincike akan lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: