Ministan harkokin noma da raya yankunan karkara Muhammad Abubakar yace, kasar nan tana da isashshen abincin da zata ciyar da mutanenta.

Ministan ya bayyana haka ne yayin jawabi akan abubuwan da gwamnatin shugaban kasa Buhari ta cimma karo Na biyar daga zuwanta kawo yanzu a wani gidan Rediyo dake Abuja jiya Litinin.
Ya kuma yi zargin cewa, tsadar abincin da ake fama dashi ya faru ne biyo bayan annobar cutar Corona, wadda tasa da yawan kasashe kulle bodojinsu ciki har da Najeriya.

Sannan yace domin samar da isashshen abinci a kasar nan, yanzu haka hukumarsa Na kokarin kafa manyan kamfanonin sarrafa shinkafa da zai sarrafa adadin ton 320 a kowacce rana.

Johohin da ake yin kamfanunuwan sun hadar da Jigawa, Kano, Adamawa, Niger, Kaduna, Gombe, Ekiti, Ogun, Bayelsa da kuma babban Birnin tarayya Abuja.
Jaridar punch ta ruwaito ministan yana cewa, suna da wadataccen abincin da zasu kula da ‘yan Najeriya kuma kullum suna Samar da abincin a duk fadin kasar nan, kuma zasu cigaba da yin hakan Dan ciyar da ‘yan kasa.
A karshe ministan ya bayyana cewa, hukumarsa na samar da babban dakin ajiyar kayan abinci mai cin ton dubu biyu a manyan ma’ajiyun gwamnatin tarayya dake Irrua a jihar Edo da kuma Ileshan jihar Osun.