Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje yayi umarnin hana matuka adaidaita sahu bin wasu daga cikin manyan titunan birnin Kano daga ranar Laraba mai zuwa.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, hana bin manyan titunan yana kunshe ne a wata sanarwa da Hukumar Kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano (KAROTA) ta fitar a safiyar yau Talata ta hannun Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa, wanda shi ne kakakin hukumar.

Sanarwar ta ce Gwamnatin jihar ta dauki wannan matakin ne bayan ta samar da titunan da manyan motoci zasu rinka bi suna daukar jama’a a kan titunan da aka hana ‘yan adaidaita bi.

Sanarwar ta kara da cewa, daga cikin titunan da aka haramtawa adaidaita sahu bi akwai titin Ahmadu Bello zuwa Mundubawa da titin Tal’udu zuwa Gwarzo.

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da cewa, ta tanadar da manyan motocin sufuri don saukakawa jama’a bin wadannan hanyoyin.

Har ila yau, KAROTA ta kara da cewa za a sanar da ranakun da masu tuka adaidaita sahu zasu daina bin karin wasu hanyoyin bayan ta samar da ababen hawa da za a yi amfani dasu a hanyoyin.

Akwai yuwuwar sake haramta bin wasu karin hanyoyin nan gaba kadan bayan samar da isassun ababen hawa da motoci da zasu wadaci al’umma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: