Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki ta barnata kusan shekaru takwas ba tare da cimma wasu abin a zo a gani ba.

Yayin da ya bayyana kusan shekaru takwas na gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin asara.
Atiku ya ce tabarbarewar mulkin jam’iyyar APC a kullum yana kara jefa ‘yan Najeriya cikin wahala.

Da yake jawabi a taron yakin neman zaben shugaban kasa a garin Akure a Jihar Ondo, ya ce ya fara kaddamar da yakin neman zabensa na shugaban kasa a shiyyar Kudu maso Yamma inda ya fara da jihar Ondo.

Dan takarar ya kara da cewa shekaru 16 da jamm’iyyar PDP ta shafe tana mulkin Najeriya ba za a iya kwatanta ta da jam’iyyar siyasar shugaba Buhari mai mulki ba.
A cewarsa, ba za a kwatanta abin da jam’iyyar PDP ta yi a cikin shekaru 16 da abin da APC ta yi a cikin shekaru 8 ba, domin kuwa APC ba su tabuka komai ba.
Yayin da yake nuna rashin aikin yi da talauci a fadin kasar, Atiku ya bayyana cewa gazawar gwamnati mai ci wajen samar da ababen more rayuwa ga ‘yan kasa ya tabbatar da gazawar gwamnatin Buhari.
Ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa na cewa idan jam’iyyarsa ta PDP ta samu nasara a zaben shugaban kasa mai zuwa a shekarar 2023, gwamnatin sa za ta kawo karshen matsalar rashin tsaro da kasar nan da ake fama da shi.