Uwargidan dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP, Titi Atiku Abubakar, ta bayyana cewa bai kamata ‘yan Najeriya su yi wa mijinta Atiku Abubakar mummunan zato ba duba da kabilar da ya fito.

A cewar Titi mijin ta Bafulatani ne kuma wayayye, ba wanda ya yi rayuwar daji ba.
Titi ta bayyana hakan ne a ranar Larabar yayin gangamin yakin neman zaben jam’iyyar da aka gudanar a Jihar Ondo.
Uwargida Titi ta ce Idan Atiku ya zama shugaban kasa, tabbas Najeriya za ta fi yadda take a yanzu domin Atiku Bafulatani ne amma ba Bafulatani na daji ba saboda shi wayaye ne domin ta sanshi sosai domin ta kasance tare da shi sama da shekaru 40.

A baya Atiku ya samu makamar aikin gwamnati, ga dukkan Yarabawa Atiku na su ne kuma shi ne zai ci zaben kasar nan inji Titi.

A nata bangaren ta bayyana kudurinta idan har ta zama matar shugaban kasa, zata kula da matasa da yara, Za kuma ta ba da tallafin karatu, don haka take shawartar ‘yan ƙasarnan da su zabi Atiku saboda ya san makamar aiki.
Da yake nashi jawabin Atiku, ya bukaci ‘yan Najeriya da kada su sake maimaita kuskuren da suka yi a shekarar 2019 a lokacin da suka zabi jam’iyyar APC mai mulki.
Atiku ya ce sun fara gangamin yakin neman zabe a Jihar Ondo a matsayin jiha ta farko a yankin Kudu maso Yamma saboda goyon bayan da suka basu.
Yace za su sanya dukkan hanyoyin gwamnatin tarayya su zama masu aiki, za kuma su ware isassun kudade ga matasa domin ayyukan yi, a cikin manufofinsu, sun ware dala biliyan 10 ga matasa, domin kuwa dole ne su ba su aikin yi.