Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Uyo na jihar Akwa-Ibom karkashin mai shari’a Agatha Okeke, ta yanke wa Albert Bassey sanata mai wakiltar Akwa-Ibom ta arewa maso gabas hukuncin daurin shekaru 42 a gida gyaran hali.

Kotun ta sameshi da laifuka 6 na karkatar da kudade da hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, ta shigar a kansa.

EFCC ta gurfanar da sanata Bassey a gaban kotun bisa zargin karbar motoci da

darajarsu ta kai Naira miliyan 204 daga wasu kamfanoni da ke da alaka da wani dan kwangila mai suna Okajide Omokore.

Omokore wanda yayin kwangilar Naira biliyan 3 ga gwamnatin jihar Akwa-Ibom, lokacin sanata Bassey ya na kwamishinan

kudi, kuma shugaban kwamitin kula da ayyukan ma’aikatu na kai-tsaye.

Laifin wanda yaci karo da sashe na 15 [2] [d] na dokar kudi ta shekarar 2011, wanda aka yiwa kwaskwarima, kana yana da hukunci a karkashin sashe na 15 [3] na ita dokar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: