Wasu yan majalisar dattijai a Najeriya sun nuna fargaba game da matakin babban kasar na takaita kudin da al’umma za su iya cire wa daga asusun ajiya.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar Philip Aduda ya janyo hankalin wakilan majalisar kan matakin da CBN din ya dauka da cewa zai iya jawo gagarumar matsala musamman al’umma masu kananan sana’o’i.
A nasa tsokacin, shugaban majalisar ta dattijai Sanata Ahmad Lawan ya ja hankalin bankin na CBN kan yin duba na tsanaki a kan al’amarin domin matakin zai shafi mutane da dama.

Sannan shugaban majalisar ya ce akwai bukatar a tattauna da bankin domin samun cikakken bayani kan tsarin, kuma ya bukaci kwamitin kula da harkar bankuna na majalisar ya tattauna kan batun a lokacin zaman tantance mataimakan shugaban bankin, wanda ake sa ran yi a mako mai zuwa.

Sabon tsarin na CBN dai na nuna cewa daidaikun mutane na da damar cire naira 100,000 ne kacal a mako, yayin da kamfanoni za su iya cire naira dubu 500 a mako.