Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce rashin tabbas game da samun kulawa bayan yin ritaya ne ke rura wutar ayyukan rashawa tsakanin ma’aikatan gwamnatin ƙasar.

Jonathan ya bayyana haka ne a jiya Talata a lokacin ƙaddamar da wani littafi game da rayuwar tsohon limamin cocin fadar gwamnatin tarayya, Obioma Onwuzurumba.
A cewar tsohon shugaban ƙasar rashin sanin makomar ma’aikata a karshen hidimarsu ga kasa na ɗaya daga cikin manyan matsalolin Najeriya, wanda ga dukkan alama shi ne ya sa rashawa ta yi katutu, wanda hakan kan jawo ma’aikatan tsintar kansu a wani hali tare da kokarin wajen sama wa kansu mafita ko ta halin ƙaƙa da nufin cigaba da kyakkyawar rayuwa bayan ritaya.

Inda ya ƙara da cewa doka ba ta bai wa ma’aikata damar yin kasuwanci ko mallakar kamfanoni ba, sannan babu wanda zai kula da kai ko yaranka bayan barin aiki.

Daga nan sai ya buƙaci masu hali su samar da wani shiri na tallafa wa tsofaffi ma’aikata, domin a cewarsa hakan zai taimaka wajen rage matsalar a fadin Najeriya.