Babban bankin Najeriya CBN ya bayyana cewa ya gabatar da sabon tsarin kudine da nufin rage tsabar kudi da ke hannun al’umma.

CBN ya bayyana cewa ba ya fito da sabon tsarin bane da nufin kuntatawa ‘yan kasa illa komawa tsarin rage yawan takardun kudi da ake hada-hada dasu a koma tsarin hada-hadar kudi ta zamani wato cashless system a turance domin karawa kudin kasar daraja wajen goyayyarsu da na kasashen waje.
Babban bankin na wannan batu ne yayin wata hira ta musamman da kafar Muryar Amurka a birnin tarayya Abuja, ta bakin daraktan hada-hadar kudi na bankin Malam Ahmad Bello Umar.

Bankin ya ce za’a fara aiwatar da komawa tsarin na’urar cire kudi ta ATM da zai rika fitar da takardun kudi daga naira 200 zuwa kasa ne daga ranar 9 ga watan Janairu na sabuwar shekara.

A cewar Bello Umar aikin mayar da na’urar cire kudi na ATM zuwa naira 200 zuwa kasa ba zai dauki dogon lokaci ba.
Ya kara da cewa ba ana son hana al’ummma cire kudinsu bane daga bankuna illa komawa tsari kan zamani, kana ya bayyana cewa idan mutum ko kamfani zai cire kudi da suka haura yadda aka kayyade to zai biya kashi biyar yayin da kamfani zai biya kashi goma.