Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da tsohuwar babbar akanta ta jihar Cross Rivers Rose Bassey da wasu mutum uku akan babbar hanyar Calaba zuwa Ogoja dake jihar.

‘Yan bindigar sun kuma harbi wani fitaccen Fasto a jihar wanda yanzu haka ken kwance a wani asibiti wanda ba’a bayyana ba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Irene Ugbo ya ce rundunar ‘yan sandan jihar ta fara aikin tantance halin da ake ciki kan lamarin.

Wannan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan da rundunar ‘yan sanda ta ce ta tura runduna ta musamman don samar da tsaro a kan babbar hanyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: