Rundunar Yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar wasu mutane hudu wadanda wasu da ake zargin yan bindiga ne su ka harbe su a jihar.

Lamarin ya faru ne a jiya Lahadi a karamar hukumar Jibiya.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Katsina SP Gambo Isah shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a yau Litinin.

Gambo Isah ya ce wasu da ake zargin yan bindigan ne suka harbi wasu mutane biyar wadanda yan kasuwa ne inda suka harbi su tare da mutuwar Hudu nan take daya kuma na karbar magani a asibiti.

Sai dai mazauna yan kasuwar yankin sun shiga firgici bisa ganin wannan lamarin da ya faru.

Karamar hukumar Jibiya ta na daga cikin kananan hukumomi ta dade ta na fama da matsalar tsaro, wadda ta kai ga har gwamnan jihar Katsina Bello masari ya nemi alummar jihar da su kare kan su.

Sai dai lamarin ya jawo ce_ce ku_ce cikin da wajen jihar har ga shugaban kasa Mahammadu Buhari ya yi magana game da lamarin kan cewa ba hurumin wani ya dauki doka a hannu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: