Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu daliban hudu a lokacin da su ke kan hanyar su ta komawa gida domin yin bukukuwan kirsimeti a Jihar Ondo.

‘Yan bindigan sun yi garkuwa da daliban ne akan titin Akunno zuwa Ajuwa da ke yankin Akoko da ke Jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa daliban suna karatu ne a kwalejin fasaha da ke Jihar Kogi a ranar Juma’a bayan yi musu kwantan bauna.

Kwamishinan rundunar ‘yan sandan Jihar shine ya bayyana faruwal lamarin ga manema labarai.

ACP Muri ya ce bayan samun labarin fariwal lamarin su ka aike da jami’an gurin domin kubtar da daliban.

Mazauna yanke da dama ne su ka shiga rudane bayan farwal lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: