Kungiyar Malaman Jami’o’i ASUU ta zargi Kakakin Majalissar wakilai Femi Gbajabiamila da yaudararsu, kungiyar tace ya bukaci su janye yajin aikin da suke Na tsawon watanni takwas a watan Oktoban da ya gabata.

Sun bayyana cewa Gbajabiamilan ya tabbatar musu cewa, anyi rubutu akan Alkawuran da gwamnati zata cika musu ba tare da bata lokaci ba in suka janye. Ciki kuwa har da biyan dukkanin albashinsu Na watanni takwas da suke bi.
Shugaban kungiyar ta Kasa Farfesa Emmanuel Osodeke ne ya bayyana haka jiya Talata a wata tattaunawa da yayi da jaridar Tribune Online. Lokacin da aka tambaye shi yaya zai bayyana shigar kakakin majalissar cikin lamarin da kuma halin da suke ciki da gwamnatin tarayya a yanzu.

Osodeke ya bayyana cewa, ASUU suna da kyakkyawan zato akan Kakakin majalissar shi yasa suka aminta da shigowarsa cikin tattaunawar dan samun mafita a matsalar da ke tsakaninta da Gwamnatin tarayya.

Ya kuma kara da cewa a lokacin Femi sai da ya nuna musu har takarda dauke da sa Hannunsa, wacce take nuna kamar dagaske ake cewa za’a bya su Albashin nasu, sannan kuma a bi sauran matsalolin a kawo karshensu.
Ya kara da cewa shigarsa ce tasa suka Janye yajin aikin, tare da burin cewa maganganunsa zasu zama aiki da cikawa. Har suka yaba masa akan kokarinsa ba tare da sanin cewa duk Yaudara bace.
Osodeke yace, su a yanzu suna kallon Gbajabiamila ne a matsayin Wanda ya yaudare su suka janye yajin Aikin, saga bisani kuma ya janye jikinsa daga cikin lamarin.
A karshe ya bayyana cewa, har yanzu Femi yana da damar da zai fito ya karyata ASUU. Ta hanyar zartar da duk Alkawuran da yayi wa kungiyar.