Rahotanni daga Jihar Anambra sun tabbatar da cewa wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun sanyawa wani Ofishin ‘yan sanda wuta a karamar hukumar Ihiala da ke Jihar.

Maharan sun yi aika-aikar ne a safiyar yau Laraba inda hakan ya sanya fargaba a zukatan mazauna yankin.
Rahotan ya bayyana cewa maharan sunje yankin ne da yawan su inda zuwan su ke da wuya su ka budewa Ofishin wuta.

A yayin harin muhimman abubuwa da dama ne na ofishin su ka kone.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar ASP Toochukwu Ikenga ya tabbatar da faruwal lamarin ta cikin wata takarda da ya fitar.
Ikenga ya ce har kawo yanzu ba su kammala gano adadin asarar da aka yi ba.
Kakakin ya ce bayan sun kammala tattara bayanin abubuwan da aka yi a sarar su za su fitar da cikakken bayani akai.