Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci babban bankin CBN da ya kara wa’adin daina karbar tsofaffin kudi har zuwa ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2023 mai kamawa.

Hakan na zuwa ne a yayin zaman zauren majalisar da ya guda a ranar Laraba wanda Sanata Ali Ndume na Jihar Borno ya karanta kudurin a gaban majalisar.
A yayin karanta kudurin Sanata Ndume ya kalubalanci bankin na CBN akan wa’adin da ya sanya.

Ndume ya ce har kawo yanzu sabbin kudaden ba su iso ga hannun mutanen cikin gari ba ballantana su isa ga hannun mutanen karkara.

Sanata Ndume ya kara da cewa matukar babban bankin na CBN bai tsawaita karbar tsofaffin kudaden ba, hakan zai jefa miliyoyin al’umma cikin wani hali.

Idan ba a manta ba Bankin na CBN ya fara fitar da sabbin kudaden ne tun a ranar 15 ga watan Disamban da muke ciki.

Daga bisani kuma bankin ya sanya ranar 31 ga watan Janairu mai kamawa a matsayin ranar da ya sanya domin daina karbar tsofaffin kudaden.

Leave a Reply

%d bloggers like this: