Gwamnatin Jihar Zamfara ta bada umarnin daukar ma’aikata 2,000 wadanda za su yi aikin yakar ta’adar shaye-shaye da daba a Jihar.

Shugaba a kwamitin yaki da daba da shaye-shaye a na Jihar Bello Bakyasuwa ne ya tabbatar da hakan a wata ganawa da manema labarai a garin Gusau babban birnin Jihar a ranar Alhamis.

Bakyasuwa ya ce gwamnatin ta bayar da umarnin daukar ma’aikata wanda su ka hada da maza da mata domin su yi aikin tabbatar da tsaron al’umma ba tare da nuna bangaranci ko siyasa ba.

Shugaban ya kara da cewa a halin yanzu mutane 6,000 ne su ke neman amma mutane 2,000 kawai za a iy dauka.

Bakyasuwa ya ce matakin daukar ma’aikatan da gwamnatin ta yi na daga cikin shirin ta fadada yaki da ayyukan daba da shaye-shaye a tsakanin matasa a dukkan fadin Jihar.

Shugaban kwamitin ya bayyana cewa baya ga aikin yakar daba da shaye-shaye, ma’aikatan za kuma su yi aikin yakar sauran laifuka daban-daban a Jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: