Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, tana binciken shugaban Jami’ar kimiyya da fasaha ta kano dake Wudil Farfesa Shehu Alhaji Musa.
![](https://matashiya.com/wp-content/uploads/2020/12/mn-1.jpg)
Hukumar Na bincikensa ne akan zargin badakalar aikin kwangila ta kimanin Naira Biliyan daya da miliyan Dari.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwato cewa, a wata takarda da ta gani hukumar ta bayyana tana binciken ne akan kwangilar da shugaban jami’ar ya bayar ta samar da kayayyakin ofisoshi da dakin karatu da kuma sanyawa ajin karatu mai daukar mutane 400 kayan amfani.
![](https://matashiya.com/wp-content/uploads/2021/10/DSC_9894-scaled.jpg)
Jaridar ta bayyana cewa bisa takardar da suka shaida, an ware Naira Miliyan 584 da Dubu 591 dan a sanya kayayyakin ofisoshi da na dakin karatu.
![](https://matashiya.com/wp-content/uploads/2020/02/matashiya-photo-2.jpg)
Sannan kuma an ware Naira Miliyan 608 da dubu 200, domin a wadata ajin Karatu mai cin mutane 400 da kayayyakin da ake bukata.
A wani bangaren kuma mai kama da wannan, kungiyar malaman jami’o’i reshen Jami’ar ta Wudil. Suna zargin shugaban makarantar da Aro kudi kimanin Miliyan 200 ba bisa ka’ida ba, Wanda aka sai motocin hawa na alfarma guda takwas.
Sannan kuma sun bayyana cewa, kuma an siyo motocin alfarmar ne kwanaki kadan bayan da gwamnati ta siyawa shugaban Jami’ar ababan hawa na Naira Miliyan 40.
Sannan kungiyar ta zargi shugaban Jami’ar Alhaji Musa da aikata ayyukan rashin gaskiya. Da yin watsi da hukunce hukuncen hukumar Jami’ar. Da kuma nuna fin karfi da iko ga kwamitin gudanar da Jami’ar.