Tsohon gwamnan jihar Adamawa Umar Jibrilla Bindow, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa Babbar Jam’iyyar Hamayya ta PDP.

Tsohon gwamnan ya bayyanawa gwamnan jihar na yanzu Ahmadu Fintiri hakan, ta hanyar tura wasu shugabannin wakilan kungiyar magoya bayansa mutum 250.

Da yake jawabi a lokacin taron da aka yi a Dakin taro na Banquet a gidan Gwamnatin jihar, Shugaban Kungiyar Abdullahi Bakari yace, sun kawo ziyarar ne bisa umarnin Jagoran nasu Bindow.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa, tsohon gwamnan ya umarci su mika masa sakon godiya ga gwamnan. Na karasa wasu ayyuka a jihar da ya gada daga wajensa.

Sannan kuma sun bayyana cikakken goyon bayansu ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, kuma Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP.

Sun bayyana cewa Atikun ya kasance shugabansu na tsawon wasu shekaru, saboda haka akwai bukatar su goya masa baya a takarar da yake ta shugaban kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: