Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana cewa ‘yan Najeriya 93,469,008 ne hukumar ta yiwa rijistar zaben shekarar 2023.

Rahotannin sun bayyana cewa mafiya yawan wadanda su ka fi yin rijistar maza 52.5% yayin da mata 47,5% ne su ka yi rijistar.

Sunayen da hukumar ta fitar na kunshe ne a jerin sunayen na karshe na wadanda su ka gudanar da rijista da hukumar ta bai wa jam’iyyun siyasa a hedkwatar hukumar da ke birnin tarayya Abuja a yau Laraba.

INEC ta ce Jihar Legas ce ke kan gaba da yawan mutane 7,060,195 ,yayin da Jihar Kano ke biye mata baya da 5,921,370 na mutane da su ka gudanar da rijistar zaben.

Hukumar ta kara da cewa Jihar Kaduna na da mutane 4,335,208.

INEC ta ce mafiya yawan wadanda su ka yi rijistar zaben matasa ne ‘yan shekara 18 zuwa shekaru 34 inda su ka zama mafiya rinjaye da 37,060,399 inda ke wakiltar kashi 39,66 na masu jefa kuri’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: