Wasu ‘yan bindiga sun hallaka shugaban kungiyar Agaji ta Fityanul Islam a Kauyen Unguwar Mai Awo ta Jihar Kaduna tare da yin garkuwa da wasu matan Aure hudu.

Shugaban matasa a yankin Adam ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.
Shugaban ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun je yankin ne da ke kusa da maraban Jos da ke hanyar Kaduna zuwa garin Zariya a Safiyar yau Labara.

Adam ya ce bayan shigar ‘yan ta’ddan yankin su ka fara harbe-harbe domin razana al’ummar yankin.

Shugaban ya kara da cewa maharan sun kuma hallaka dan uwa ga shugaban kungiyar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar SP Muhammad Jalige ya bayyana cewa zai bincike daga bisani kuma zai bada cikakken bayani.