Akalla mayakan Boko Haram 377 suka ajiye makamansu a yankin Arewa maso Gabas.

 

Tubabbun mayakan sun hada da maza 52 da mata 126, sai kuma kananan yara 199.

 

Ya ce, dakarun sun kubutar da fararen hula 47 da aka yi garkuwa da su.

 

Mayakan Boko Haram da ISWAP 377, ciki har da mata da kananan yara daga sassa daban-daban a yankin sun mika wuya.

 

Hakan ya faru ne yayin samamen da rundunar Operation Hadin Kai ta kai kan mayakan a yankin.

 

Daraktan yada labarai na sojoji, Manjo-Janar Musa Danmadami ne ya bayyana haka ranar Alhamis a Abuja yayin taron manema labarai da suka shirya.

 

Jami’in ya kara da cewa, sun samu nasarar kashe wasu mayakan ISWAP yayin farmakin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: